IQNA

Makarancin Kur’ani Da Iran Ya Lashe Gasar Mafaza

23:58 - June 15, 2018
Lambar Labari: 3482762
Bangaren kasa da kasa, dan kasar Iran ne ya lashe gasar mafaza ta tashar alkawsar ta talabijin da maki 84.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Ali Asgar Shu’a’i dan kasar Iran ne ya lashe gasar mafaza ta tashar alkawsar ta talabijin da maki 84 da aka gudanar karo na goma sha daya.

Muhammad Fathulla Bibaras dan kasar Masar ya zo na biyu da maki 82.5, sai Muhammad Taqi Awari 81, Muhammad Aldulhadi Shuhaimi 75.5 daga Lebanon, Malek Dalfi 75 daga Iraki.

Dukkanin adadin mutanen da suka halarci gasar ya kai 113 daga kasashe 20, kuna an gudanar da gasar ne kamar yadda aka saba ta hanayar talabijin, amma daga karshe mutane iyar suka kai matain karshe.

Wannan dai ita ce gasar kur’ani mafi girma a talabijin da ake gunarwa a duniya, wadda mutane daga kasashe suke shiga.

3722934

 

 

 

captcha