Kamfanin dillancin labaran iqna, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana hakan ne a yau din nan Juma'a a wata ganawa da yayi da manyan jami'an kasar Iran da kuma jakadun kasashen musulmi da suke Tehran bugu da kari kan dubun dubatan al'ummar Iran da suka kai masa ziyarar barka da salla inda ya ce daya daga cikin mafiya muhimmancin daukakar da al'ummar musulmi suke da ita shi ne hadin kan da suke da shi.
Ayatullah Khamenei ya ce babbar siyasar ma'abota girman kan duniya ita ce kokarin wajen haifar da rarrabuwan kai tsakanin musulmi, don haka sai ya ce: hanya guda kawai ta fada da wannan siyasa ta Amurka da sahyoniyawa ita ce fahimtar makircinsu da kuma tsayin daka wajen fada da hakan.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya kara da cewa daya daga cikin manufofin samar da haramtacciyar kasar Isra'ila ita ce haifar da sabani da rikici tsakanin musulunci, to sai dai ya ce dukkanin alamu suna nuni da cewa ba za ta taba dawwama ba, don haka sai ya kirayi shugabanni da masana da masu fadi a ji na duniyar musulmi da su ba da himma da kuma sauke nauyin da ke wuyansu a wannan bangaren.