IQNA

An Fara Gudanar Da Gasar Kur’ani Da Sunnah Ta Kasa Da Kasa A Indonesia

22:31 - March 20, 2018
Lambar Labari: 3482491
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da gasar kur’ani ta kasa da kasa a birnin Jakarta fadar mulkin kasar Indonesia.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Arab yaum cewa, a jiya an fara gudanar da gasar kur’ani da sunnar annabi (SAW) ta kasa da kasa a birnin Jakarta fadar mulkin kasar Indonesia tare da halartar wakilai daga kasashe 25 na duniya.

Wannan gasa za ta mayar da hankalia  bangarori biyar ne, da suka hada da bangaren karau, da kuma hardar kur’ani, sai kuma bangaren hadisan manzon Allah (SAW.

Daga karshe za a bayar da kyautuka ga mutane uku da daya da na biyu da na uku a dukkanin bangarorin gasar, daga cikin yautukan da za a bayar ga wadanda suka zo na daya har zuwa aikin hajjin bana.

3701509

 

 

 

 

 

 

captcha