IQNA

Kungiyar Jihadul Islami Ta Yi Kira Zuwa Ga Babbar Zan-zanga Domin Kare Quds

22:31 - December 15, 2017
Lambar Labari: 3482204
Bangaren kasa da kasa, kungiyar ta Jihadul-Islami ta fitar da sanarwar gayyatar dukkanin Paladinawa da su fito kwansu da kwarkwatarsu a ranar Juma'a domin kare birnin Kudus da masallacinsa.

Kmafanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kungiyar ta Jihadul-Islami na yin Zanga-zanga a ranar juma'a 15 ga watan Decemba.

Kiran dai ya zo ne a daidai lokacin da  al'ummar paladinu take ci gaba da gudanar da Zanga-zangar nuna kin amincewa da matsayar Amurka akan birnin kudus.

A gefe daya, sojojin haramtacciyar Kasar Isra'ila sun kai hare-hare akan yankuna daban-daban na palasdinu a lokacin da al'ummar Palasdinu ke gudanar da Zanga-zanga a garin Bethlehem da Isawiyyah.

Tun ranar laraba 6 ga watan Decemba ne dai shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana birnin Kudus a matsayin babban birnin haramtacciyar Kasar Isra'ila.

3672831

 

 

 

 

 

 

 

captcha