Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa shugaban karamin ofishin jakadancin Iran a kasar Senegal ya rubuta wata Makala kan muhimmancin hadin kan alummar musulmi wadda aka buga a jaridar Direct Info.
Sayyid Hassan Esmati a cikin makalar tasa ya yi nuni da cewa, ko shakka hadin kai na da gagarumin tasiri da kuma gudunmawa wajen ci gaban al'umma da zaman lafiyarta, kamar yadda hakan zai amfanar da musulmi da masauran al'ummomin da suke tare da su.