IQNA

Ammar Hakim:

Isra’ila Ce Kawai Za Ta Ci Ribar Rarraba Kasashen Musulmi

20:41 - October 13, 2017
Lambar Labari: 3481995
Bangaren kasa da kasa, shugaban jam’iyyar Hikma a kasar Iraki ya bayyana yunkurin rarraba kasashen msuulmi da cewa shiri ne wanda Isra’ila za ta ci riba da shi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na Saumaria News cewa, Ammar hakim shugaban jam’iyyar Hikma a kasar Iraki ya bayyana yunkurin rarraba kasashen msuulmi da cewa shiri ne wanda Isra’ila za ta ci riba da shi kuma wannan dama shirinta ne.

Ya ci gaba da cewa, tun bayan da aka fara haifar da rikici a cikin yankin gabas ta tsakiya na yaki a tsakanin al’ummomi a cikin shekaru biyar zuwa shida da suka gabata ya zuwa, babu wata kasar muuslmi da ta ci ribar abin da yake faruwa.

Dangane yunkurin tarwatsa kasashen msulmi da sunankafa wasu kasashe kuwa, ya bayyana cewa wannan shirin dama can akwai shi, kuma ahalin yanzu ne aka fara tunanin aiwatar da shi.

Daga cikin kasashen da ake son a rarraba kuwa dama akwai siriya, bayan ta kuma sai Iraki, yakin da aka hadasa a cikin siriya somin tabi ne na wannan shiri da makiya musulmi suka shirya.

3652156


captcha